<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>36</hymn_number>
<title>Mu Zo da Murna Dayawa LW36</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mu zo da murna dayawa,
 mu ta da muryarmu,
 Mu rera waƙa sabuwa,
 waƙar mala'iku.

[V2]
 2) Ubangiji ya cancanci
 ya karƃi yabonmu.
 Gama lalle ya rinjayi
 Shaiɗan makiyinmu.

[V3]
 3) Ya cancanta, Mai Cetonmu,
 ya karƃi albarka.
 Shi ne ya mutu dominmu,
 ya ka da mutuwa.

[V4]
 4) Albarkaci Ubangiji,
 ku talikansa duka.
 Mai iko ne, mai girma shi,
 yanzu, har abada.</lyrics>
</song>